An kwantar da Mandela a asibiti

Nelson Mandela
Image caption Tsohon Shugaban Afrika ta Kudu

An kwantar da tsohon shugaban Africa ta Kudu, Nelson Mandela a asibiti bayan da cutar huhun da ya ke fama da ita ta sake taso masa.

Wata sanarwar da aka fitar ta ce an kai tsohon Shugaban Africa ta kudun mai shekaru casa'in da hudu a duniya asibiti ne, jim kadan gabanin karshe goma sha biyu na daren jiya.

Sanarwar ba ta bayar da wani Karin bayani ba, illa dai cewar tsohon shugaban na samun kyakkyawar kulawa daga kwararrun likitocin da ake da su a kasar.

Nelson Mandela wanda a shekara ta 1994, ya zama shugaban Africa ta Kudu bakar fata na farko, ya dade yana fama da laulayi, ga kuma yawan shekaru.

Ko a farkon wannan watan sai da aka kwantar da shi a asibiti na dan wani lokaci domin duba lafiyarsa.

A watan watan Disamba ma ya shafe kusan makwanni ukku a asibiti, saboda ciwon huhu da kuma tiyata da aka yiwa matsarmamarshi.

Kwanciyar da yayi ta watan Disamba dai ita ce mafi tsawo da ya taba yi a asibiti, tun bayan da aka sallame shi daga cikin kaso a sheakara ta 1990, bayan ya shafe kusan shekaru talatin a gidan yari.

An daure shi ne bisa laifin hada baki domin hambarar da gwamnatin farar fata 'yan tsiraru ta mulkin wariyar launin fata.

Shugaba Mandela dai yana da tarihi na rashin lafiyar huhu, tun daga lokacin da ya kamu da cutar tarin fuka a gidan kurkuku.