Fararen hula sun dauki mataki a Mexico

Image caption Kungiyoyin yan banga na kara tasiri a Mexico

Daruruwan fararen hula ne dauke da makamai a kasar Mexico su ka kama wasu mutane goma sha biyu kuma suka mika su ga hukuma a garin Tierra Colorado dake kudancin kasar.

Cikin wadanda aka kama har da wani shugaban al'umma wanda aka zarga da taimakawa wata gungun kungiya.

Wannan dai shine aikin taimako kai mafi girma a Mexico tun da aka fara samun kungiyoyin sa kai dake bullowa domin kare al'umma a farkon wannan shekara.

Al'ummar kasar dai sun fara gajiya da miyagun kungiyoyi wadanda su ka addabi rayuwarsu ta hanyar sace-sace da kuma kashe-kashe.

Hakan ne kuma yasa su ka tashi tsaye domin kare al'umominsu inda suke sintiri akai- akai suna kafa shingaye domin binciken masu safarar miyagun makamai, a garin Tierra Colorado dake yammacin jihar Guerrero.

An dai kashe wani shugaban al'umma ne a farkon wannan makon bayan ya nuna adawarsa da irin danniya da kuma cin hanci da 'yansanda ke karba.

A yanzu haka dai kungiyoyin 'yan banga na tasiri a garuruwa da dama a Mexico musamman ganin yadda aka samun aikata manya laifuka kuma jami'an tsaro basa iya tabukka katabus.

Sai dai wasu jihohin basu amince da ayyukan kungiyoyin ba amma dai ya zuwa yanzu ba su dauki matakin wargaza su ba.