Plato: an kashe mutane 27

A Najeriya rahotanni daga yankin Bokkos da ke jihar Pilaton na cewa, an kashe akalla mutane ashirin da bakwai,wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon wani sabon rikici da ya barke.

Wasu mazauna yankin na cewa 'yan kabilar Ron ne suka kai wa Fulani hari.

A 'yan kwanakin nan dai ana dada samun rikice-rikicen kabilanci da na addini a jihar ta Pilato bayan an samu sararawa ta wani lokaci.

Jihar Pilato dai ta kwashe fiye da shekaru goma tana fama da tashin hankali dake da nasaba da addini da kuma kalbilanci.