Saudiyya zata sa ido a kan Twitter

Image caption Abdallah, sarkin Saudiyya

Masarautar Saudi Arabiya tana ƙoƙarin hana ɓadda sawu da wasu masu amfanin da shafin faɗi-sonka na Twitter ke yi ta hanyar tabbatar da cewa, ba wanda zai iya amfani da shafin na Twitter acikin ƙasar har sai ya tabbatar da ko shi waye.

Wannan dai mataki ne da zai baiwa masarautar Saudiyyan damar sa ido akan irin ra'ayoyin da wasu masu amfani da shafin na Twitter ke bayyanawa.

Shafin na Twitter dai yana da farin jini sosai a kasar ta Saudiyya, kuma 'yan kasar suna yi amfani da shafin wajen yin muhawara akan batutuwan da da suka hada da addini da kuma siyasa.

Koda acikin makon da ya gabata masarautar Saudiyyan ta buƙaci kamfanonin waya su sa, ido, ko kuma ma su toshe shafin Skype wanda ke baiwa jama'a damar yin magana da juna da kuma ganin juna ta vidiyo kyau.