An yankewa Vlahovic hukuncin daurin shekaru 45

Vlahovic
Image caption Veselin Vlahovic zai shafe shekaru 45 a Kurkuku

Wata kotu a Bosnia ta yankewa wani kwamandan mayakan Sabiya hukuncin daurin shekaru 45 a kurkuku, saboda laifin gallazawa fararen hula a Sarajevo lokacin yaaki a shekarun 1990.

Veselin Vlahovic wanda ya kasance tamkar fir'auna a birnin Grbavica, an same shi da laifin kisan kai, da fyade da kuma azabtar da Musulmin Bosnia da fararen hula 'yan Croatia.

Alkalai sun bayyana shi a matsayin wanda ke jin dadin kashe mutane.

Bayan yaaki dai, an kama Vlahovic da laifin fashi da makamaki a kasar Montenegro amma sai ya gudu daga gidan kaso ya arce zuwa kasar Andalus wato Spain.

A shekara ta 2010 ne aka sake damke shi, aka kuma tasa keyarsa zuwa Bosnia.