Za'a tura dakaru 3000 Congo

Image caption Fararen hula da dama ne ke rasa rayukansu a rikicin na Congo

Kwamitin tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya ta amince da a girke jami'an tsaro domin yakar 'yan tawaye a Jamhuriyar Demkradiyyar Congo.

Dakarun za su taimakawa sojojin kiyaye zaman lafiya ne na Majalisar Dinkin Duniya da ke tabbatar da zaman lafiya a kasar wato MONUSCO.

Sakatare Janar din Majalisar ya ce yana fata matakin da kwamitin ya dauka zai farfado da gwamnati a kasar da kuma daurewar zaman lafiya.

Dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ba su tabba aiwatar da aikin kai hare-hare ba a ayyukanta.

Amma sama da mutane miliyan biyar ne su ka rasa rayukansu a rikincin da ya ki ci yaki cinyewa a Congo inda kungiyoyi dauke da kamai suke kaiwa junansu harei.

Kungiyar na baya-baya nan ita ce yan tawayen M-23. Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na ganin tura dakaru dubu uku kasar domin yakar 'yan tawayen zai taimaka wajen rage kisan fararen hula a kasar.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce fararen hula a koda yaushe suna cikin hadari ne a kasar.

Bayan an kawar da barazanar da 'yan tawayen suke wa al'ummar kasar, Majalisar ta ce zata zartar da kudurin domin samar da sojoji na musamman da za su rika tafiyar da al'amuran tsaro a kasar.