Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga:Dokar hana amfani da leda

Image caption Tsibin ledoji

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta mika wa Majalisar dokoki wani kudurin dokar dake neman haramta amfani da leda ko yin ta a kasar ko kuma ma shiga da ita cikin kasar.

Shin ya ya al'amarin yake a wajenku? Kuna ga ya kamata hukumominku su kafa irin wannan doka?

Wadannan da ma sauran batutuwa na daga cikin abun da muka tattauna a filinmu na Ra'ayi Riga na wannan mako!