An bukaci kasashen Koriya su maida wukar

korea
Image caption Shugaba Kim Jung-un ya ce suna shirin ko-ta-kwana

Kasashen China da Rasha sun yi gargadin cewar rikici mai hadarin gaske na konno kai a kan iyakar Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu, inda suka bukaci bangarorin biyu su maida wukar.

Ministan harkokin wajen Rasha, Sergie Lavrov ya ce matsalar za ta iya fin karfin kowa, kuma batun zai iya dagule al'amura.

Lavrov yace " A wannan yanayin, muna cikin damuwa tare da martanin da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya dauka dama kasashen duniya, kuma mataki na yin gaban kai na janyo karuwar ayyukan soji da zai janyo matsaloli".

China dai ta dade tana bayyanawa bangarorin biyu su maida wukar.

Karin bayani