Bankuna sun soke bashin 'yan siyasa a Cyprus

Image caption Bankin Cyprus na cikin bankunan da suka yafewa 'yan siyasa bashi

Wasu Kafofin yada labarai a Girka sun buga jerin sunayen 'yan siyasa a Cyprus wadanda ake zargi an soke bashin da bankuna ke binsu.

Wannan lamari ne dai ake kyautata zaton ya jefa tattalin arzikin kasar cikin rudani.

Bankin Cyprus da Laiki da kuma Hellenic sun yafewa kamfanoni da hukumomin kasar da kuma 'yan siyasa makudan kudaden da suke bin su.

Tuni dai aka mika jerin sunayen ga majalisar dokokin Cyprus din domin gudanar da bincike.

Shugaban kasar ta Cyprus, Nicos Anestesiyades ya ce yana ganin duk da rudanin da aka samu a kasar, abubuwa sun dai-daita.

Ya ce yakamata kowa ya rungumi matakin da aka dauka a kasar.

Karin bayani