Ba'a gano masu rai ba a Tibet

Image caption Sama da ma'aikatan ceto dubu daya ne aka tura sansanin hako ma'adanan

Yan kasar China fiye da tamanin da kuma masu aikin hakar ma'adinai yan kasar Tibet ne ake fargabar sun rasa rayukansu, bayan da kasa ta rufta musu a Tibet.

Masu aikin ceto dai sun ce har yanzu ba su ga alamun akwai wani mai rai da ya rage ba a cikin wadanda kasar ta rufta musu a Lhasa, babban birnin Yankin Tibet.

Kafofin yada labarun gwamnatin China sun ce yansanda dubu daya, da ma'aikatan kwana-kwana da kuma likitoci aka tura inda lamarin ya faru.

Ma'aikatan da lamarin da ya rutsa da su dai suna yiwa babban kamfanin hakar zinare na China aiki ne.

Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Juma'a amma ba'a samu bayanai ba sai da yammacin ranar Juma'a.