An soki gwamnatin Najeriya

buhari
Image caption Tsohon Shugaban Najeriya, Janar Muhammadu Buhari

Dan takarar shugabancin Najeriya karkashin jam'iyyar adawa ta CPC a zaben da ya gabata, Janar Muhammadu Buhari yace kamata yayi a dauko warware matsalar Boko Haram tun daga tushe.

Janar Buhari ya kuma ce, babu wata alaka tsakanin addini da hare-haren ta'addanci da ake fuskanta yanzu haka a arewacin Najeriya.

Jigon na 'yan adawar Najeriya ya kuma ce matsalar 'yan ta'adda ba wai ta tsaya ne a arewacin Najeriya ba, kuma matsalar tsaron ma baki daya wata alama ce ta gazawar shugabanci a kasar.

Janarar Buhari ya ce hakki ne na gwamnati ta fahimci yadda 'yan kungiyar boko haram suka fara kuma a san yadda za a yi da su.

Ya kuma ce akwai bukatar ganin cewa gwamnatin tarayya ta yi kokarin sanin ko su wanene yan kungiyar ta boko haram.

Karin bayani