Shugaba Issoufou na kokarin samarda ruwa a Damagaram

isuor
Bayanan hoto,

Shugaban Nijer, Alhaji Mahamadou Issoufou

Shugaban kasar Nijar Alh Mahamadou Issoufou ya aza tubalin aikin samar da wadatatun ruwan sha a jahar Damagaram.

Al'ummar ta Damagaram dai ta dade tana fama da wannan matsala hakan ne yasa a shekara ta dubu biyu da biyar gwamnatin waccen lokacin ta samar da madatsar ruwa ta Arunguza da kwararru suka ce sai Damagaram ta kwashe shekaru hamsin ba tare da ta sake fuskantar wannan matsala ba sai dai shekaru biyu bayan hakan matsalar ta dawo .

Yanzu kuma hukumomin cewa suka yi da wannan aiki na arewacin Ganaram sai an kwashe shekaru dari da talatin da biyar ba tare da wannan matsala ta karancin ruwa ta dawo ba.