Paparoma Francis ya yi bukin Easter

Image caption Paparoma Francis

Paparoma Francis yayi amfani da bukukuwan ranar Easter na farko da ya gabatar akan mukaminsa wajen yin kiran a samar da zaman lafiya a duk fadin duniya.

Yayin jawabin da ya gabatar ga dubban masu ibada da suka yi tururuwa a dandalin St. Peter dake birnin Rome, sabon Paparoman yayi kiran a samar da mafuta ta diplomasiyya dangane da zaman dar-dar dake karuwa a yankin Korea.

Paparoman ya kuma ambato irin rikice-rikicen da ake fama da su a yankin gabas ta tsakiya da kuma nahiyar Afurka.

Jagoran cocin Roman Katolikan ya kuma nuna takaici dangane da safarar mutane da kuma muggan kwayoyi.