Obama ya gabatar da bayanan nazartar kwakwalwar bil Adama

Shugaba Obama na gabatar dan bayanai kan nazartar kwakwalwar bil Adama
Image caption Shugaba Obama na gabatar dan bayanai kan nazartar kwakwalwar bil Adama

Shugaban Amirka Barack Obama ya gabatar da cikakken bayanai kan wani gagarumin sabon yunkurin Amirka na nazartar kwakwalwar bil Adama.

Mr Obama ya baiyana shirin wanda ya kwatanta shi da zayyana taswirar kwayoyin hallitar dan Adam da nasabarsa, yana mai cewa wannan wani abin al'amara dake jiran baiyanarwa.

Obama yace makasudin binciken shine domin gano hanyoyin magani da kuma warkar da cutattuka da dama wadanda suka hada da cutar Alzheimer dake haddasa mantuwa mai tsanani da kuma cutar Parkinsons dake shafar kwakwalwa da sa karkarwar jiki.