Sojan Pakistan sun kashe masu tayar da kayar baya

Sojojin Pakistan cikin shirin kai farmaki
Image caption Sojojin Pakistan cikin shirin kai farmaki

Rundunar sojan Pakistan tace, an kashe masu tada kayar baya su goma sha biyar da kuma wani jami'in tsaro guda yayin da soja suka kaddamar da wani sabon babban farmaki a yankin Tirah, dake arewa maso yammacin lardin Khyber.

Sojan gwamnatin Pakistan dai sun kwashe fiye da mako guda suna kokarin kawar da masu tada kayar baya na kungiyar Taliban daga yankin.

Cikin kwanakin da aka kwashe ana fada a yankin ya zuwa yanzu, an kashe masu tda kayar baya fiye da dari, kuma soja ashirin sun rasa ransu.

Dubban fararen hula ne dai suka gudu da yankin da ake gwabza fada.