An yi wa wata yar jarida fyade a Brazil

Brazil police
Image caption Ofishin yan sanda na mata a Brazil

Yan sanda a Brazil sun ce an yi wa wata mata dake yawon bude ido fyade da kuma sata a cikin wata karamar motar bus a Rio de Janeiro, birnin da zai karbi bakwancin gasar kwallon kafa na duniya da za a yi a shekara mai zuwa da kuma gasar wasani na Olympics a shekarar 2016.

Sai dai yan sanda sun ce sun kama mutane biyu ciki harda direban motar.

Yan sandan sun ce mutanen sun sa sauran fasinjoji fita daga motar a lokacinda da suka ga baturiyar wacce ke tare da saurayinta kuma sun shiga motar ne a unguwar Copacabana a birnin Rio.

Wakilin BBC ya ce direban ya wuce da motar wajen garin birnin kuma an yi wa matar fyade ne a lokacin da motar ta bi kan wata gada a birnin na Rio yayinda aka daure hanun saurayinta kuma aka lakada masa duka daga bisani kuma aka ajiyesu a wajen garin na Rio bayan da aka tilasta masu amfani da kartin siyaya a shago don cire kudi daga naurar ATM.

Fashi a cikin motocin bus- bus ba sabon abu bane a birnin Rio de Janeiro sai dai irin karfin da aka yi amfani da shi da kuma nuna isa ya ba kafafefen watsa labarai mamaki.