An hallaka mutane 19 a Jihar Kaduna

Kaduna
Image caption Kaduna

Rahotanni daga Jihar Kaduna a Nigeria sun ce mutane akalla 19 ne suka rasu wasu 10 kuma suka sami munanan raunuka yayin da wasu 'yan bindiga suka kai hari yankin Attakar na karamar hukumar Kaura a kudancin jahar ta Kaduna.

Bayanai dai na nuna cewa kauyuka 2 na yan kabilar Attakar wannan al'amari ya shafa inda a yanzu mutane da dama ke gudun hijira a wasu kauyuka da ke makwabtaka.

Ko a kwanan baya dai sai da aka sami rikici a wannan yanki tsakanin Fulani mazauna da kuma yan kabilar ta Attakar.

Karin bayani