An kashe dan Najeriya a Timbuktu

mali
Image caption Ana bata kashi a Mali

Rahotanni sun nuna cewar tashin hankalin da ake yi a Timbuktu na kasar Mali, ya rutsa da wani dan Najeriya wanda ya rasu sakamakon tashin bam na dan kunar bakin wake.

Bayanai sun ce yanzu haka, sojojin kasar Faransa da na Mali na can suna ci gaba da fafatawa da 'yan tawayen Islama a birnin Timbukutu.

A ranar Lahadi an yi kazamin fada tsakaninsu inda aka ce an hallaka 'yan tawaye kusan ashirin da kuma sojan Mali guda.

Wani dan kunar bakin wake ne dai ake jin ya tarwatsa bam a wani wurin da sojojin kasar Mali suke.

Karin bayani