Mutane 6000 sun hallaka a fadan Syria

Syria
Image caption Syria

Wata kungiyar dake fafutuka a Syria ta ce, an kashe a kalla mutane dubu shida a watan daya gabata, fiye da kowane lokaci tun bayan da aka fara bore a kasar shekaru biyu da suka wuce.

Kungiyar ta kara da cewa kashi daya bisa uku na mutanen da aka kashe fararen hula ne.

Kungiyar ta Syrian Observatory for Human Rights wacce ke Burtaniya, ta ce tana da bayanan da ke nuna yadda bangarorin dake yaki a Syrian ke keta hakkokin bil'adama.

Mai magana da yawun kungiyar, ya shaidawa BBC cewa adadin mutanen dake mutuwa na ci gaba da karuwa sakamakon karuwar tashe- tashen hankula a kasar.