Birtaniya ta yi garan bawul a tsarin lafiya

camerob
Image caption Pirayi Minista David Cameron

Gwamnatin Birtaniya ta bullu da wasu sabbin garan bawul a kan tsarinta na kiwon lafiya da kuma tallafin gwamnati ga jama'a.

A sabon tsarin, likitoci a Ingila sune zasu dunga lura da kasafin kundinsu, tare da bada damar kara gasa tsakanin takwarorinsu wajen samarwa jama'a abubuwan lafiya.

Sai dai masu suka sunce tsarin tamkar sayarda kaddarorin gwamnati ne ta bayan fage.

A sauyin da aka yi wajen bada tallafi kuwa, gwamnati za ta rage tallafin data ke baiwa mutanen da ke zaune a gidajen gwamnatin wadanda keda dakuna a cikin gidajensu wanda basa amfani dasu.

A cewar gwamnati wannan tsarin zai bada dama ga wadanda iyalansu keda yawa su koma manyan gidaje.

Karin bayani