Francois Bozize ya zargi gwamnatin Chadi

Francois Bozize
Image caption Francois Bozize

Tsohon shugaban kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya Francois Bozize da yanzu ke samun mafaka a kasar Camaro ya yi magana ne gabanin taron shugabannin yankin da za a yi yau a birnin Ndjamena babban birnin kasar Chadi

Ya ce sun wahala tun harin farkon da mayakan yan tawaye na kungiyar SELEKA su kai a ranar goma ga watan disemba da kuma wanda suka kai ranar ashirin da uku da kuma ashirin da hudu ga watan Maris din daya gabata.

Mr Bozize ya kuma ce ya yanke shawarar yin murabus ne bayan da su ka yi magana da jakadan Faransa a wayar taraho domin kaucema tashin hankali.

Sai dai tsohon shugaban kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya ya zargi gwamnatin kasar Chadi da nuna goyon baya ga yan tawaye.

Ya ce sun tabbatar cewa mayakan kungiyar SELEKA sun sami goyon bayan dakaru na musaman na kasar Chadi da suka kai wa barikin soja na kasar Afrika ta Kudu hari a ranar ashirin da hudu ga watan Maris

Mr Bozize ya kuma ce ya so ya halarci taron shugabannin yankin amma gwamnatin Chadi ta nuna rashin amincewarta game da haka.