Ana taron warware rikicin CAR

Image caption Sabbin shugabannin jamhuriyar tsakiyar Afurka

Yau ne shugabannin ƙungiyar bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen yankin Afrika ta tsakiya suke tattaunawa akan halin da ake ciki a jamhuriyar Afurka ta tsakiya tun bayan juyin mulkin da 'yan tawaye na SELEKA suka yi.

Ana dai yin taron ne a birnin N'Djamena na ƙasar Chadi, yayin da tsohon shugaban kasar Afurka ta tsakiyar, Francois Bozize ya zargi Chadin da taimakawa 'yan tawayen da suka hamɓarar da gwamnatinsa.

Mr Bozize wanda ke gudun hijira a Kamaru ya shaidawa BBC cewa sojojin Chadi sune suka jagoranci farmakin karshe na boren yan tawayen wanda ya hada da harin da aka kaiwa sansanin sojin Afirka ta kudu dake kasar.