Amurka za ta tura makaman kariya zuwa yankin Koriya

Chuck Hagel, Sakataren tsaron Amurka
Image caption Chuck Hagel, Sakataren tsaron Amurka

Ma'aikatar tsaron Amirka ta ce za ta tura ingantattun makaman kariyar makamai masu linzami zuwa yankin Guam nan da yan makonni masu zuwa a matsayin riga kafin barazana daga Koriya ta arewa da kuma kare kasar Amirka daga dukkan wani farmaki.

Sakataren tsaron Amirka Chuck Hagel ya yi kashedin cewa take taken baya bayan nan na Koriya ta arewa lamari ne dake da matukar hadari da Amirka da kawayenta Koriya ta kudu da kuma Japan.

Yace Amirka na aiki tare da China da kuma sauran kasashe wajen kwantar da hankula a yankin na Koriya.

Tun da farko a yau Koriya ta arewa ta hana daruruwan ma'aikata yan Korita ta kudu wucewa zuwa wurin aiki a yankin masana'antun hadin gwiwar kasashen biyu dake kan iyaka a yankin arewaci.

Pyongyang ta yi barazanar kaddamar da yaki tare da alkawarin sake habaka makamanta na nukiliya.

Tun farko dai Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce Amurka ba za ta amince da dadin bakin koriya ta Arewa na baya bayanan ba.

Ya ce abun da shugaba Kim Jong Un ke son ya yi tamkar tsokanar fada ce da ke da hadari kuma Amurka ba za ta amincewa Koriya ta Arewa ta zaman kasar da ta mallaki makamin nukliya ba.

A jiya talata gwamnatin Koriya ta arewa ta sanar cewa za ta farfado da tasharta ta nukliya da kan iya samarda kayayyakin harhada makaman kare dangi.

Ha kuma lamarin na zuwa ne a dai dai lokacinda Koriya ta Kudu ta ce koriya ta arewa ta dakatar da jigilar daruruwan 'yan kasar Koriya ta kudu dake aiki a wani yanki na masana'antu da ke kan iyaka.

Karin bayani