Za a bada tukwuicin kama shugabannin LRA

Image caption Amurka ta bada tayin tukwuici kan kama shugabannin LRA

Amurka ta ce za ta ba da tukwuicin dala miliyan biyar, ga duk wanda ya ba da labarin da zai kai ga cafke jagoran kungiyar tawaye ta Lord's Resistance Army watau Joseph Kony.

kony, shi ne ya jagoranci tawaye a Uganda har kusan shekaru ashirin, wanda kuma kotun kasa da kasa ke nema ruwa-a-jallo, bisa zargin aikata laifukan yaki.

Wani babban jami'i a ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya ce kungiyar ta LRA ce ke da alhakin kisan mutanen da aka yi bila-adadin da sassare wa wasu sassan jiki da kuma mayar da wasu bayi.

Tun farko kasar Uganda ta ce, ta jinginar da farautar Joseph Kony da take yi a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, saboda gabar dake tsakaninsu da sabuwar gwamnatin da ke can.

Karin bayani