An yi addu'o'in zaman lafiya a Kano

kwnakwaso
Image caption Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso

Da safiyar ranar Alhamis ne aka gudanar da addu'o'i a masallatan Juma'an na kananan hukumomin jihar Kano dake arewacin Nigeria domin neman Allah ya kawo zaman lafiya a kasar.

A babban Masallacin Juma'a na Kano dai an gudanar da addua'ar ne karkashin jagorancin limamin Kano, yayin da Sarkin Kano da kuma gwamnan jihar suka kasance cikin daruruwan jama'ar da suka halarci addu'ar.

Jihar ta Kano dai ta jima tana fama da matsaloli na tsaro, musamman a 'yan kwanakinnan da lamuran suka kara muni.

A cewar mahukuntan jihar dai da kuma malamai babu abin da zai kawo karshen mastsalar sama da addu'a.

Karin bayani