korea ta arewa ta amince ta yaki Amurka

Image caption Korea ta arewa ta shirya yaki da Amurka

Korea ta Arewa ta ce ta ba sojojin ta amincewar karshe su kaddamar da hari a kan Amurka abin da ya hada da yiwuwar amfani da makaman nukiliya.

Babban hafsan mayakan kasar a Pyongyang ya ce a shirye kasar take ta kai mummunan hari a matsayin wani martani, ga abin da ta kira barazana ta gangan da Amurka ke yi wa kasar.

Ma'aikatar tsaron Amurka ta yi tir da wadannan kalamai, a jerin kalaman tsokana daga Korea ta Arewa.

Janar Richard B Myers shi ne kwamanda na sojojin Amurka a Japan a shekarun 1990, ya kuma ce tun shekaru da dama da suka wuce sojojin Amurka sun jaddada bukatar zama cikin shiri na barkewar rikici a yankin na Korea.

Yace, "Ko da yaushe cikin damarar yaki muke, sojojin kuma da za mu tura Korea a kowanne lokaci zaune suke a cikin shiri.

Karin bayani