An kafa kwamitin duba afuwa ga 'yan Boko Haram

Image caption Najeriya ta nada kwamitin yiwa Boko Haram afuwa

Gwmnatin Najeriya ta kafa kwamiti da zai duba yiwuwar aiwatar da shirin afuwa ga 'yan kungiyar jama'atu ahlis sunnah lidda'awati wal jihad da wasu ke kira boko haram.

Wannan yunkuri dai tamkar amsa kiraye-kirayen da wasu 'yan kasar suka yi ta yi a 'yan kwanakin nan ne, game da muhimmancin yin afuwar.

A baya dai gwamnatin Najeriyar ta ce ba za ta aiwatar da shirin afuwar ba sai 'yan kungiyar sun dakatar da hare-haren da suke kaiwa tare da fitowa fili don sanin ko su wane ne.

Aniyar gwamnatin Najeriyar ta aiwatar da shirin yi wa 'yan kungiyar jama'atu ahlis sunnah liddawati wal jihad afuwa dai ta fara fitowa ne, bayan wata ganawar da shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan ya yi da wasu dattawan kasar karkashin jagorancin dan masanin Kano, Dr Yusuf maitama Sule.

Sai dai za iya cewa maganar ta kara karfi sakamakon kiran taron majalisar tsaron kasar da shugaban Najeriyar ya yi, inda bayanai suka nuna an kafa kwamitin da zai duba yiwuwar aiwatar da shirin afuwar.

Kwamitin zai duba hanyoyin da zai bullo ta yadda shirin afuwar zai hada da dukkan 'ya'yan kungiyar da sauran wadanda lamarin ya shafa.

Bayanai sun nuna an bai wa kwamitin makwanni biyu domin ya gabatar da shawarwarinsa ga majalisar tsaron Najeriyar.

Karin bayani