An dakatar da bada agaji a Gaza

Image caption Hukumar bada agaji ta dakatar da aiyukanta a Gaza saboda zanga-zanga

Majalisar Dinkin Duniya za ta dakatar da aiki a dukkan cibiyoyin ta na rabon agajin abinci dake Zirin Gaza.

Hakan ya biyo bayan afkawa daya daga cikin cibiyoyin da masu zanga-zanga dake nuna rashin amincewar su da zaftare kasafin kudin suka yi.

An dai shafe kusan mako guda ana zanga-zanga a Gaza.

Hukumar rabon agajin na bayar da agajin abinci ga Palasdinawa 'yan gudun hijira kimanin dubu dari takwas a Gaza, kuma ta bayyana abin da ya faru a matsayin wani abin damuwa kuma abin mamaki saboda muninsa.

Karin bayani