Yunkurin shawo kan matsalar tsaro a Najeriya

Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram
Image caption Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya kafa wani kwamiti da zai duba yiwuwar yi wa 'yan kungiyar Jama'atu AhlusSunna Lidda'awati wal Jihad, da akafi sani da Boko Haram afuwa.

Matakin ya biyo bayan wani taro gaggawa na tsaro da Shugaba Jonathan ya jagoranta kwana guda bayan ganawarsa da wasu dattawan arewacin Najeriya, wadanda suka bukace shi ya dauki matakan kawo karshen zubar da jini a cikin kasar.

A baya dai shugaba Jonathan ya kekashe kasa akan cewar ba zai yiwa 'yan Boko Haram afuwa ba.

Tuni masana harkokin tsaro, sun fara tofa albarkacin bakinsu game wannan yinkuri domin lalubo bakin zaren warware matsalolin tsaro a arewacin kasar.

Karin bayani