An tuhumi Bubo na Gunea Bissau da laifin safarar kwayoyi

Image caption Tsohon Babban hafsan sojin ruwan Guinea Bissau na fuskantar tuhumar safarar kwayoyi

Tsohon babban hafsa na mayakan ruwan Guinea Bissau dake Yammacin Afrika Hose Americo Bubo Nacuto ya gurfana a gaban wata Kotun Newyork dangane da zargin safarar miyagun kwayoyi.

Rear Admiral din wanda aka fi sani da Bubo a kasar sa an tuhume shi ne da sauran wasu mutanen da ake zargin suna hada baki a wajen rarraba hodar iblis da ake kaiwa kasar Amurka.

Wasu jami'an leken asiri ne na Amurka da suka yi shigar-burtu suka kame Nacuton a wani samame da suka kai a yankin teku dake Yammacin Afrika.

An kuma tuhumi wasu daga cikin mutanen da aka kama tare da shi da laifukan ta'addanci saboda alakar da suke da ita da kungiyar 'yan tawaye ta FARC dake kasar Columbia.

Karin bayani