Za a sake tattaunawa da Iran kan nukiliya

Image caption Za a shiga rana ta biyu kan tattaunawa da Iran

Wakilan manyan kasashen duniya masu shawarwari za su koma zaman tattaunawa da kasar Iran a game da shirin ta na nukiliya bayan sun kammala zama a ranar farko ba tare da cimma wata yarjejeniya ba.

Wakilan kasar Iran sun ce sun riga sun zayyana bayanai masu mahimmanci da kuma shawarwari na zahiri a tattaunawar da aka yi a Kazakhstan.

Mataimakin babban wakilin Iran a wajen shawarwarin Ali Bagheri ya ce, kasar ta Iran ta rigaya ta bayar da shawarar yadda za a aiwatar da shirin da aka tsara a Rasha.

To amma wani jakadan kasashen Yammacin duniya ya ce Iran din ba ta bayar da wata amsa takamaimai ba a kan tayin baya-bayan nan da manyan kasashen duniyar da suka hada da Amurka da Birtaniya da Rasha suka yi mata na sassauta mata wani bangare na takunkumin karya tattalin arziki da aka garkama mata, idan dai har ta amince ta daina aiki a wasu sassa na shirin nukiliyar ta da ake ganin suna da hadari.

Karin bayani