An sallami Mandela daga asibiti

Image caption Nelson Mandela, tsohon shugaban Afurka ta kudu

An sallami tsohon shugaban ƙasar Afurka ta Kudu, Nelson Mandela daga asibiti, inda ya yi jinyar cutar huhu da a Turance ake ƙira, Pneumonia.

Mandela dai ya kwashe kwanaki goma ana yi masa magani a asibiti.

Gwamnatin Afurka ta kudu ta fitar da wata sanarwa da ke cewa, Mandela ɗan shekaru casa'in da huɗu, yana samun sauƙi, kuma za'a cigaba da yi masa magani a gida.

Mandela wanda ya shafe shekaru ashirin da bakwai a gidan yari, ya jagoranci kawo ƙarshen mulkin wariyar launin fata a Afurka ta kudu.