Mutane sama da 30 sun mutu a hadari a Najeriya

Image caption Najeriya na kara samun yawaitar hadurra

Jami'ai a Najeriya sun ce mutane fiye da talatin ne suka mutu a wani karo da aka yi tsakanin wata motar Safa da tankar mai a kudancin kasar.

Gobarar da ta tashi kuma bayan karon wadda ta dauki sa'oi biyar tana ci ta kurmushe gidajen dake kusa da kananan motoci.

Akasarin mutanen da suka mutu suna cikin babbar motar safarar ne.

Hadarin dai ya faru ne a Kauyen Igbo-gui dake cikin jihar Edo a kan babban hanyar da ta hada Lagos da jihohin dake kudu maso gabashin Najeriya.

Karin bayani