Najeriya: 'Yan sanda sun musanta ikirarin MEND

'Yan kungiyar MEND
Image caption Kungiyar MEND a yankin Niger Delta a Najeria

A Najeriya rudunanr 'yan sandan ƙasar reshen jihar Bayelsa dake yankin Niger-Delta ta musanta ikirarin da ƙunguiyar MEND mai fafutuka ta yi cewa, ta hallaka 'yan sanda goma sha biyar.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Bayelsa yace, harin da ya kai ga salwantar 'yan sanda goma sha biyu rikici ne tsakanin wasu tsoffin masu tada ƙayar baya.

'Yan sandan sun kuma ce, sun gano ko su waye suka kai harin kuma zasu kamo su.

Ƙungiyar MEND ta fitar da wata sanarwa inda tace, ita ta hallaka 'yan sanda goma sha biyar yayin harin a jihar Bayelsa.

MEND ta kuma ce ta kai harin ne domin nunawa rundunar haɗin gwiwa ta JTF daka yankin cewa da gaske suke akan batunsu na sake komawa kai hare-hare.

A ranar Alhamis ne dai ƙungiyar ta MEND ta yi barazanar sake komawa kai hare-hare bayan da wata kotu a Afurka ta Kudu ta yankewa ɗaya daga cikin shugabanninta, wato Henry Okah hukuncin ɗaurin shekaru 24 a gidan kaso.

Karin bayani