Margaret Thatcher ta Rasu

Margaret Thatcher
Image caption Margaret Thatcher

An bada sanarwar mutuwar tsohuwar Firayi Ministar Birttania, Margaret Thatcher. Margaret Thatcher ta rasu tana da shekaru tamanin da bakwai a duniya.

Tsohuwar Priyi Ministar ta taka muhimmiyar ruwa a siyasar duniya. Ta dade tana fama da rashin lafiya.

Kakakin tsohuwar Firayi ministar ya ce ta rasu ne bayan da ta samu bugun jini a safiyar yau.

A matsayinta na macen farko da ta zama Firayi Minista a Brittania, Margaret Tatcher ta sauya fasalin siyasar Birttania tun daga lokacin da ta hau kan karagar mulki a shekara ta 1979

Karin bayani