Ana cigaba da alhinin mutuwar Thatcher

Margaret Thatcher
Image caption Margaret Thatcher

Masu alhinin mutuwar Margaret Thatcher, tsohuwar Firaministar Biritaniya, suna can suna ajiye furanni a kofar gidanta.

Kana an saukar da tutoci kasa-kasa a gine-ginen gwamnatin kasar.

Firaministan Biritaniya na yanzu, David Cameroon, ya yaba mata a matsayin Firaminista mace ta farko a Biritaniyar, kuma tsohuwar shugaban jam'iyyarsa ta Conservative.

Sauran wadanda suka yi nasu yabon ga Mrs Thatcher har da shugaban Amurka, Barack Obama, da tsohon shugaban Afrika ta Kudu, F W de Klerk, da kuma shugabar Liberia, Ellen Johnson Sirleaf, wadda ta ce Margaret Thatcher ta karfafawa mata gwiwar shiga a dama da su a harkokin siyasa.

A yau da hantsi ne dai Margaret Thatcher ta rasu, tana da sheakaru tamanin da bakwai a duniya.

Ta rasu ne bayan ta sha fama da ciwon bugun jini.

Karin bayani