An kai hari a Ingawa dake Jihar Katsina

Image caption Jami'an yansandan Najeriya na fuskantar hare-hare daga yan bindiga

A Najeriya, a daren ranar Litinin ne wasu yan bingida da ba a san ko sa waye ba, su ka kai hari a Ofishin 'yan sanda dake karamar hukumar Ingawa da ke jihar Katsina.

Mazauna karamar hukumar Ingawa da ke jihar katsina wadda ke arewa maso yammacin Najeriya sun ce sun wuni a daren ranar Litinin suna ji karar harbe-harben bindigo a garin.

Wani mazauni garin wanda yake kusa da Ofishin 'yansandan da yan bindigan su ka kai hari ya shaidawa BBC cewa sunji karar harbe-harbe na kusan mintuna talatin.

Kwamishinan yan sandan Jihar Katsina, Abdullahi Magaji ya tabbatarwa BBC da aukuwar lamarin, amma ya ce maharan ba su kai ga isa ofishin yansanda ba kafin a kora su.

Ya ce yansanda dake gadin ofishin sunyi nasarar korarsu, kuma har yanzu suna kan bincike.

Sai dai bai tabbatar da asarar rayuka ko jikkata ba, a yayinda ya ce gabatar da cikakken bayanai ga manema labarai a kan abun da ya faru a yau Talata.