Uhuru Kenyatta ya yi rantsuwar kama aiki

Shugaba Uhuru Kenyatta
Image caption Shugaba Uhuru Kenyatta

An rantsar da Uhuru Kenyatta a matsayin sabon shugaban kasar Kenya na hudu.

Hakan ya biyo bayan nasarar da ya samu a babban zabe na kasa da aka yi a watan Maris.

Haka kuma kotun kolin kasar ta tabbatar da nasararsa, bayan abokin takararsa Raila Odinga ya shgar da kara yana kalubalantar sakamakon zaben.

Shugabannin kasashen Afrika da jami'an Diplomasiyar kasashen yamma da yawa ne suka halarci bukin tare da dubban 'yan kasar ta Kenya a filin wasanni na Nairobi.

Mr. Kenyatta da mataimakinsa, William Ruto dai na fuskantar tuhuma a kotun hukunta manayan laifuka ta duniya.

Ana tuhumarsu ne da iza wutar tashin hankalin da ya biyo bayan zaben da aka yi shekaru biyar da suka wuce a kasar.

Mr. Kenyatta wanda ya taba takarar shugabancin kasar a shekarar 2002 da bai yi nasara ba, da ne ga tsohon shugaban kasa Jomo Kenyatta.

Ra'ayoyin mutane sun bambanta game da ko tasirin mahaifinsa ne ya sanya shi yin nasara a siyasa, ko kuwa fafutukarsa ta siyasa ce ta sa ya yi nasarar kasancewa shugaban kasar ta Kenya.

Karin bayani