Masana'antar hadin gwiwa ta daina aiki a Korea

Image caption Ma'aikatar hadin gwiwa ta Gaesong

Ma'ikatan kasar Koriya ta arewa ba su zo aiki ba a wata masana'antar hadin gwiwa tsakanin Korea ta Arewa da ta kudu a Gaesong bayan gwamnatin a Pyongyang ta ce ta dakatar da ayyuka a yankin.

Masana'antar hadin gwiwar tsakanin kasashen biyu, wani yinkuri ne na kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Kusan shekaru goma kenan masana'antar hadin gwiwa tsakanin Korea ta arewa da ta kudu ke aiki duk da zaman dar-dar din da ake yi a yankin Korea da kuma hare-haren soji.

A yanzu haka dai an dakatar da alamar duk wata dangantaka tsakanin kasashen biyu bayan ayyuka sun tsaya cik a masana'antar.

Kusan ma'ikata kasa da dari biyar 'yan kasar Koriya ta kudu ke aiki a cibiyar, kuma suna nan zaune ba kayan aiki da kuma abokan aikinsu daga kasar Koriya ta arewa.

Pyongyang dai ta rufe kan iyakar ta ne da Kudu a ranar Laraban da ta gabata.

Gwamnatin kasar ta Koriya ta kudu ta yi watsi da matakin da Koriya ta arewa ta dauka a yayinda ta ce Koriya ta arewa na da alhakin abun da ya faru.

Amma Kasar Koriya ta arewa za ta fi fuskantar koma baya saboda dakatar da ayyukan a cibiyar.

Sama da 'yan kasar dubu hamsin ne ke aiki a ma'aikatar, kuma cibiyar na taimakawa gwamnatin kasar da kudaden shiga.