An samu ci gaba wajen rage hukuncin kisa- Amnesty

Image caption Kungiyar Amnesty International ta ce ci gaba da yunkurin ganin a rage aiwatar da hukuncin kisa

An samu ci gaba wajen rage hukunci kisa- AmnestyKungiyar kare hakkin dan-adam ta Amnesty International ta ce tana ci gaba da yunkurin da take yi wajen ganin an daina yanke hukuncin kisa a duniya.

Sai dai kuma, kungiyar ta ce ta damu kwarai ganin yadda wasu kasashe suka koma suna amfani da irin wannan hukunci.

Kasashen sun hadar India wacce ta zartar da irin wannan hukunci a shekarar 2004, haka ma Japan da Pakistan da kuma Gambia.

Kungiyar ta cigaba da cewa kasar China na amfani da wannan hukunci, amma a boye, sai dai ta ce ta yi amannar cewa an aiwatar da wannan hukunci akan mutanen kasar da dama.

Haka ma a kasar Iran, kungiyar ta ce tana ankare, saboda zartar da irin wannan hukunci na karuwa.

Duk da karuwar yanke irin wannan hukunci a wasu kasashen duniya, kungiyar ta Amnesty international ta ce akwai ci gaba a kokarin da ake na hanawa aiwatar da hukuncin kisa