Girgizar kasa ta hallaka mutane 37 a Iran

iran
Image caption Girgizar kasa tayi barna a Iran

Akalla mutane talatin da bakwai suka rasa rayukansu, yayinda fiye da mutane dari takwas da hamsin kuma suka jikkata a wata girgizar kasa da ta faru a birnin Bushehr inda Iran ke da tasharta kwaya daya tilo ta makamashin nukiliya.

Girgizar kasar wadda mizaninta ya kai awo shida da digo uku wadda kuma da'irar karfinta ya kai tazarar kilomita dari a kudu maso gabashin birnin, an jiwo amonta har cikin Dubai da Abu Dhabi da kuma Baharain.

Gwamnan jihar Bushehr Fereydun Hasanvand ya bada kiyasin mutanen da lamarin ya ritsa da su da kuma ta'adin da girgizar kasar ta haifar.

Gwamnan yace" girgizar kasar ta faru ne kamar misalin karfe hudu da minti ashirin da biyu, kuma mutane talatin da biyu suka rasu yayin da wasu kimanin dari takwas da hamsin suka sami raunuka. Gidaje kimanin 700 suka rugurguje."

Karin bayani