Majalisar Birtaniya na neman ayi sulhu da Taliban

Image caption Za'a janye sojojin Burtaniya a Afghanistan a shekara ta 2014

Kwamitin tsaro na Majalisar dokokin Birtaniya ya nuna damuwa, game da samar da da ingantaccen tsaro a kasar Afghanistan, bayan kasashen duniya sun janye dakarunsu a kasar.

Kwamitin ya ce kasar na iya fadawa yakin basasa, cikin wasu 'yan shekaru masu zuwa.

Kwamitin dai ya bukaci gwmnatin Birtaniya ta janye dakarunta a kan lokaci amma ta bukace ta da ta yi amfani da matsayinta a duniya wajen ganin an dai-daita al'amura a kasar kafin karshen shekara ta 2014.

'Yan Majalisa dai sun ce gwamnatin Birtaniya na da alhakin da ya rataya a wuyanta na ganin an daidaita al'amura a Afganistan kuma an inganta tsaro a kasar kafin karshen shekara ta 2014, lokacin da Burtaniya za ta janye sojojinta daga kasar.

Sunce sojojin hadaka na kasashen waje da ke Afganistan sun gaggara rage yawan tashe-tashe hankulan da ake samu a kasar, kuma hakan na dakile ci gaba tattalin arzikin yankin.

Kwamitin tsaro na Majalisar ya ce dolene a hau teburin sulhu da kungiyar taliban inda ana so a samar da zaman lafiya a Afghanistan.

Kwamitin ya ce muddin ba a yi haka ba kasar na iya shiga yakin basasa cikin wasu yan shekaru masu zuwa.

Har wa yau 'yan Majalisar sun nuna damuwa game da kwarewar dakarun Afganistan musamman wajen amfani da jirage masu saukar angulu da kuma samar da agaji na asibiti kafin shekara ta 2015.

Sakataren harkokin tsaron Birtaniya Philip Hammond ya ce a yanzu haka sojojin Afghanistan ne ke tafiyar da sama da kashi tamani na harkokin tsaro a kasar, inda ya ce kasar na kan hanyarta na samarwa kanta tsaro.