Bakin haure na yin tururuwa zuwa Brazil

Bakin hauren Haiti a Brazil
Image caption Galibin bakin hauren dake zuwa Brazil 'yan Haiti

Gwamnatin Brazil ta kira wani taron gaggawa dangane da karuwar bakin haure dake tudada zuwa kasar daga Bolivia.

Ministan shari'a na jihar Acre, dake cikin kurmin Amazon yace, bakin hauren sun fito ne daga kasashe masu nisan gaske da suka hada da Bangladesh, da kuma Najeriya, amma galibinsu sun 'yan Haiti ne.

Ministan ya kuma ce, a yanzu jihar ta Acre ta zama wani babban zangon shige-da-fice da 'yan sumogal suke iko da shi.

Tun bayan girgizar kasar da aka yi a shekara ta 2010 ne dai ake samun karuwar 'yan kasar Haiti dake tururuwa zuwa Brazil, kuma sune mafi yawan leburorin dake aikin gine-ginen da za'a yi amfani da su wajen daukar bakuncin gasar wasan kwallon kafa ta duniya da za'a yi a shekara ta 2014 a birnin Rio de Janeiro.