Limamin Yahudawa ya shiga matsala

Babban limamin Yahudawan Faransa, yayi murabusa daga mukaminsa bayan ya amsa ya saci rubuce-rubucen da wani yayi, da kuma yin karya akan karatun da yayi.

Wannan badakala dai ta fito fili ne bayan wata mujalla ta wallafa labarin dake cewa, limamin Yahudawan, Gilles Bernheim ya gatabar da rubutun da wani yayi a matsayin nasa.

Koda Paparoma Benedict da yayi murabus ya ambato wani bangare na rubutun da limamin Yahudawan yayi akan auren jinsi guda, amma daga baya aka gano cewa, ya dauka wannan bayani ne daga rubutun da wani malamin cocin Roman Katolika yayi.

Limamain Yahudawan ya kuma amsa cewa, yayi karya da yace, yayi karatu a jami'ar Sorbonne dake birnin Paris.