'Yan gudun hijirar kasar Mali na shan wahalaa Mauritania- Kungiyar MSF

'Yan gudun Hijirar kasar Mali
Image caption 'Yan gudun Hijirar kasar Mali

Kungiyar likotocin agaji ta duniya ''Medecins Sans Frontiers'', ta koka kan mawuyacin halin da 'yan gudun hijirar kasar Mali ke fuskanta a kasar Mauritania.

Kungiyar ta ce dubban 'yan gudun hijirar da ke gujewa matsalar rashin tsaro a arewacin Mali na fama da rashin lafiya a yayin da suke isa sansanin Mbera, wajen da ya kamata a ce sun samu taimako da tsaron lafiyarsu.

Kungiyar ta kara da cewa kananan su suka fi jin jiki inda akasarinsu ke fama da matsalar yunwa inda lamarin yafi muni ga wadanda suka fice tun bayan da sojoji karkashin jagorancin Kasar Faransa suka fara kaddamar da hare-haren kan 'yan tawaye da suka mamaye yankin.