Michel Djotodia ya zama shugaban kasa

Majalisar gudanar da mulki da aka kafa makon jiya a jamhuriyar Afurka ta Tsakiya ta zabi jagoran 'yan tawaye, Michel Djotodia a matsayin shugaban rikon kwaryar na kasar.

Shi dai Michel Djotodia ya nada kansa a matsayin shugaban kasar bayan da dakarun 'yan tawayen suka kwace iko da Bangui babban birnin kasar, a juyin mulkin da ya sa shugaba Fransuwa Bozize tserewa daga kasar.

Yanzu haka dai jama'a a duk fadin kasar musamman a manyan birane na fatan zabar jagoran 'yan tawayen a matsayin shugaban kasar zai sa yanayin tsaro ya inganta a kasar.