Hukumar IMF ta farfado da dangantakarta da kasar Somalia

Shugabar Hukumar IMF, Chritine Lagarde
Image caption Shugabar Hukumar IMF, Christine Lagarde

Hukumar bada lamuni ta duniya IMF ta farfado da dangantaka tsakaninta da gwamnatin Somaliya, bayan da ta yanke hulda da kasar har na tsawon shekaru 22.

Sake farfado da dangantakar dai zata sa hukumar taimakawa kasar da tsare-tsare da kuma shawarwari.

To sai dai kuma hukumar ba zata baiwa Somaliyar rance ba har sai kasar ta biya hukumar dinbim basussukan da take binta, da ya kai kimanin dala miliyan dari uku da hamsin.

Hukumar ta IMF dai ta farfado da hulda tsakaninta da sabuwar gwamnatin Somaliyar ce, tun bayan da shugaba Hassan Sheikh Mohamud ya dare kan karagar mulki a bara.