An samu koma baya a shari'ar Mubarak

An kawo karshen soma sake yin shari'ar tsohon shugaban kasar Masar, Hosni Mubarak cikin ruɗani yayin da alkalin dake jagorantar shari'ar ya sanar da cewa, ya janye daga shari'ar.

Alkalin, Mustafa Hassan Abdullah ya bayyana janyewar tasa ne jim kaɗan bayan an shigar da tsohon shugaba Mubarak, da 'ya 'yansa biyu cikin akurkin wadanda ake tuhuma a kotu sai alkalin kotun, abunda ya zowa jama'a da bazata.

Da yawan Misirawa dai na ganin wannan wani babban koma baya ne ga shari'ar da akewa tsohon shugaban kasar.

Kuma yanzu haka wasu daga cikin Misirawa sun fara dawowa daga rakiyar shugabancin Mohammed Morsi.