Ahmadinajad ya fara ziyara a Afrika

Image caption Ahmadinajad na ziyara a kasashen Afrika uku

Shugaban kasar Iran, Mahmud Ahmadinejad, ya isa Jamhuriyar Benin a farkon ziyarar da ya fara zuwa kasashe uku a Nahiyar Afrika, wadanda suka hada da Ghana da Jamhuriyar Nijar.

Shugaba Ahmadinejad dai ya yi kokarin kulla huldar zumunci da kasashen Afrika yayin da yake mulki.

Kasar farko da ya fara ziyarta da ganawa da Shugaban kasar ita ce Mali, kwanaki kalilan bayan samun nasara a watan Yuni na shekara ta dubu biyu da biyar.

Shugaba Ahmadinajad, nan da wasu 'yan watanni ne zai kammala wa'adin mulkinsa a kasar.

Karin bayani