Fashewa a Boston, Amurka, ta hallaka mutane biyu

Boston
Image caption Boston

'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar akalla mutane biyu, ashirin da uku kuma suka sami raunuka, a fashewar abubuwa da aka samu a daidai layin da ake kammala tseren gudun yada-kanen-wani na Boston.

Akwai kuma wasu rahotanin da ke cewa, wasu abubuwa biyu masu karfin gaske sun fashe a birnin Boston din na Amurka.

Wasu hotuna da ake nunawa kai tsaye daga wurin da lamarin ya faru, sun nuna mutane jinajina, ma'aikatan kiwon lafiya na yi masu magani.

Motocin daukar marasa lafiya masu yawa da na 'yan sanda da kuma na jami'an kashe gobara sun isa wurin, domin bada agaji.

An yi wa Shugaba Obama bayanin fashewar. Kana an kara daukar matakan tsaro a manyan gine-gine na birnin New York.